Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya ruwaito cewa: Mujallar Foreign Policy ta ce Iran tana ɗaukar wannan yaƙi a matsayin wani lamari mai alaƙa da rayuwarta da tsaron ƙasarta, don haka Tehran a shirye take ta jimre wa tsadar yaƙi da matsin lamba na dogon lokaci. Sabanin haka, Amurka duk da tunaninta na farko, ba ta iya samun nasarar gaggawa da ƙudurcewa da take fata ba.
Mujallar a cikin rahotonta ta ce hauhawar farashin mai da iskar gas a duniya, matsin tattalin arziki a cikin Amurka, adawa a Majalisar Wakilai, da raguwar goyon bayan jama'a sun jefa gwamnatin Trump cikin ƙalubale masu tsanani.
A cikin nazarin an kuma kawo cewa ’yan siyasar Amurka har yanzu suna gujewa amincewa da yarda da haƙiƙanin abin da ke faruwa a ƙasa, waɗanda suka haɗa da ƙarfin juriyar Iran da iyakokin ƙarfin sojan Amurka.
Bisa ga rahoton, matuƙar Washington ba ta ɗauki wata manufa ta haƙiƙa ba kuma ta ci gaba da dagewa kan dabarun “matsin lamba mafi girma” da kuma canjin tsarin mulki a Iran, to fita daga wannan yaƙi zai kasance mai wuyar gaske kuma mai tsada sosai gareta.
Foreign Policy ta kuma amsa a fakaice cewa juriyar Iran ta ƙalubalanci manufofin yaƙin gwamnatin Trump sosai, kuma ta jefa Amurka cikin wani hali inda babu sauki ga kaiwa ga nasara, haka nan kuma babu fita daga rikicin ba tare da biyan wata azababbar asara mai yawa ba.
………………………………………..
Your Comment